Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKu ajiye makamai ku dawo cikin al’umma – Gwamna Radda ga yan...

Ku ajiye makamai ku dawo cikin al’umma – Gwamna Radda ga yan bindiga

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga ’yan bindigar da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da su ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta bai wa duk wanda ya tuba da gaske damar komawa cikin al’umma tare da fara sabuwar rayuwa mai amfani.

Ya ce manufar gwamnatin ita ce dawo da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma, ba tare da ware kowa ba.

Radda ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da gidaje 152 da aka gina wa mutanen da rikicin tsaro ya raba da muhallansu a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Ya ce samar da gidajen wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa waɗanda rikice-rikicen tsaro suka shafa tare da sake gina rayuwarsu bayan shekaru na wahala da ƙaura daga matsugunansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments