Jami’an ’yan sanda a yankin Peel da ke lardin Ontario na kasar Canada sun kama wani tsohon kyaftin din jirgin saman Air Canada mai suna Geoffrey Wall bisa zargin amfani da takardun lasisin tukin jirgin sama na bogi.
A cewar hukumomin tsaro, an kama Wall mai shekaru 59 ne bayan gudanar da bincike na tsawon watanni hudu kan sahihancin takardunsa da cancantarsa a harkar tukin jiragen sama.
’Yan sanda sun ce an gurfanar da shi kan laifukan damfara da wasu tuhume-tuhume masu alaka da harkokin sufurin jiragen sama.
Binciken ya nuna cewa Wall ya jagoranci zirga-zirgar jirage sama da 900 na cikin gida da na kasa da kasa tsakanin shekarar 2009 zuwa 2025, yayin da ake zargin ya yi amfani da takardun lasisin bogi wajen gudanar da aikinsa.
Rahotanni sun ce duk da cewa yana da sahihin lasisin tukin jirgin kasuwanci, bai mallaki Airline Transport Pilot Licence (ATPL) ba, wanda shi ne mafi girman lasisin da ake bukata domin mutum ya zama kyaftin din jirgin sama.
Hukumomi sun bayyana cewa bincike na ci gaba da gudana domin gano yadda aka bari wannan lamari ya dauki tsawon lokaci ba tare da an gano matsalar ba, tare da tantance ko akwai wasu kura-kurai a tsarin tantance cancantar matuka jiragen sama.