Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira da a gaggauta yin cikakken garambawul ga tsarin tsaron Najeriya.
Sanata Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa matsalar rashin tsaro na ƙara muni a faɗin ƙasar duk da dimbin kuɗaɗen da ake kashewa a fannin tsaro.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a X a ranar Talata, Kwankwaso ya nuna matuƙar damuwa kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga, satar mutane, ta’addanci, rikicin ƙabilanci da fashi da makami a sassa daban-daban na ƙasar.
“Na damu da ƙaruwar matsalar rashin tsaro da ta mamaye ƙasarmu.”
Tsohon gwamnan ya ambato jihohi kamar Zamfara, Borno, Sokoto, Katsina, Kwara da Oyo a matsayin wuraren da matsalar ta fi kamari, yana mai cewa yawancin ’yan ƙasa ba sa iya “barci da idanu biyu a rufe.”
Kwankwaso ya kuma bayyana damuwa kan ƙaruwar ƙarfin gwiwar ƙungiyoyin masu aikata laifi, yana mai cewa suna amfani da kafafen sada zumunta wajen yin wulakanci ga hukumomi da kuma tsoratar da jama’a.
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne ƙarfin gwiwar waɗannan masu laifi, waɗanda yanzu suke yin amfani da shafukan kai-tsaye domin yi wa hukumomi ba a da kuma tsoratar da jama’a,” in ji shi.
Ya kuma kafa hujja da gogewarsa a matsayin tsohon gwamna da ministan tsaro, yana mai cewa matsalolin tsaro ba abin da ba za a iya shawo kansa ba ne.
“A matsayina na wanda ya yi wa ƙasa hidima a matakai daban-daban, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano da Ministan Tsaro, inda muka fuskanci kuma muka rage matsalolin tsaro ta hanyar shugabanci mai ƙarfi da haɗin gwiwar al’umma, ina ganin cewa rashin tsaro ba abin da ya fi ƙarfin a shawo kansa ba ne,” in ji shi.
A cewarsa, matsalar ba rashin kuɗi ba ce, sai dai ƙarancin kwarin gwiwar shugabanni wajen tunkarar rashin tsaro da ƙarfi.
Ya ce tsarin da ake bi yanzu bai kawo sakamakon da ake so ba duk da manyan kasafin kuɗi da ake warewa fannin tsaro, yayin da ake ci gaba da rasa rayuka da kuma raba dubban iyalai da gidajensu.
Kwankwaso ya yi kira da a inganta walwala da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, a ƙara inganta tattara bayanan sirri, a ƙarfafa tsaron al’umma (community policing), tare da magance tushen matsalar rashin tsaro.
Ya kuma bukaci gwamnati ta ƙara zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, wutar lantarki, noma, koyar da sana’o’i da samar da ayyukan yi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage talauci da rashin aikin yi da ke haifar da rashin tsaro.