Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya rantsar da sabbin ministoci biyu a Abuja

Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci biyu a Abuja

Joseph Tegbe da Ambasada Sola Enikanolaiye sun karɓi ragamar sabbin muƙamansu bayan rantsarwa.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gudanar da bikin rantsar da Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin sabon Ministan Wutar Lantarki, yayin da Ambasada Sola Enikanolaiye ya zama Karamin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, inda sabbin jami’an suka yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban ƙasar.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.

Sabbin nade-naden na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na ƙarfafa gudanar da ayyukan ma’aikatun gwamnati tare da inganta ayyukan da suka shafi samar da wutar lantarki da kuma hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya.

Ana sa ran sabbin ministocin za su fara aiki nan take domin ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu a bangarorinsu daban-daban.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments