Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage kuɗaɗen gudanar da ayyukan yau da kullum da ake ware wa ministoci zuwa Naira 700,000.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage kashe kuɗaɗen gudanarwa tare da tabbatar da amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa sabon tsarin zai shafi yadda ma’aikatun gwamnati ke tafiyar da wasu ayyukan yau da kullum, inda ake sa ran zai taimaka wajen rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.