Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKarancin wuta: An lalata manyan turakun wutar lantarki 6 a Nasarawa

Karancin wuta: An lalata manyan turakun wutar lantarki 6 a Nasarawa

Kamfanin kula da rarraba Wutar Lantarki na Najeriya, ya sanar da cewa wasu bata-gari sun lalata manyan turakun wutar lantarki guda 6 da ke kan layin Apir zuwa Lafia a Jihar Nasarawa, lamarin da ya janyo tangardar samar da wutar lantarki a wasu yankuna.

A cewar kamfanin, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar 30 ga Mayu yayin da ake fama da ruwan sama mai ƙarfi.

Bayan katsewar layin, an yi yunƙurin dawo da wutar ta hanyar amfani da wani layi na daban, amma hakan bai yi nasara ba.

Babbar Manajar Hulɗa da Jama’a ta TCN, Ndidi Mbah, ta ce jami’an kamfanin sun gano cewa an yi barna a turakun wutar lantarkin guda shida, abin da ya haddasa matsalar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments