Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeBa zan yi murabus ba, zan ci gaba da jagoranci muddin ina...

Ba zan yi murabus ba, zan ci gaba da jagoranci muddin ina raye – Shugaban kasar Iran

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya musanta rade-radin da ke cewa yana shirin ajiye mukaminsa, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da jagorantar ƙasar muddin yana raye.

A cikin wani bidiyo da kafar yada labarai ta Tasnim News Agency ta wallafa, shugaban ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin murabus duk da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Pezeshkian ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen fuskantar kalubalen da ke gabanta, yana mai cewa ko dai za su yi nasara a kan manufofinsu ko kuma su sadaukar da rayukansu a wannan tafiya.

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa yana tunanin sauka daga kan mulki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments