Dakatar da karatu ya janyo cikas a makarantun gwamnati a jihar Oyo bayan kungiyar malaman makarantu ta NUT ta umarci malamai su shiga zanga-zanga domin nuna damuwa kan sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya samo asali ne bayan wasu masu ɗauke da makamai sun kai hari makarantu uku da ke ƙauyukan Esiele da Yawota a ranar 15 ga Mayu, 2026, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai.
Tun bayan aukuwar lamarin, al’umma a sassa daban-daban na Najeriya sun ci gaba da nuna fushinsu tare da kira ga hukumomi da su gaggauta kubutar da waɗanda aka sace.
Bincike ya nuna cewa umarnin NUT ya haifar da dakatar da harkokin karatu a makarantun gwamnati da ke ƙananan hukumomi 33 na jihar Oyo.
Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce nuna goyon baya ga waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane tare da jan hankalin gwamnati kan halin da suke ciki.
Ya ce an sanar da shi batun yajin aikin ne ta waya daga shugabanninsa, lamarin da ya sa ya bar wurin aikinsa domin bin umarnin kungiyar.
Shi ma wani malamin ya ce zanga-zangar wata hanya ce ta nuna alhini da tausaya wa ɗalibai da malamai da suka kwashe sama da makonni biyu a hannun masu garkuwa da su.