Annobar cutar kwalara ta yi sanadin rasuwar sama da mutum 40 tare da jefa fiye da mutane 3,000 cikin rashin lafiya a wasu sassan jihar Borno a watan Mayun 2026.
Rahotanni sun nuna cewa cutar ta bulla a kauyuka da unguwanni 139 da ke cikin kananan hukumomi bakwai na jihar, ciki har da Maiduguri, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri.
A cewar Daily Trust, annobar ta bazu ne tsakanin ranar 1 zuwa 28 ga watan Mayu, inda alkaluman gwamnati suka nuna cewa yawan mace-macen ya karu daga mutum 27 zuwa sama da 40 cikin kankanin lokaci, yayin da adadin masu dauke da cutar ya zarce 3,000.
Sai dai wasu iyalan wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa alkaluman na iya kasancewa kasa da hakikanin adadin, suna masu cewa akwai mutane da dama da suka rasa rayukansu a gidajensu ba tare da sun samu damar zuwa asibiti ba.