Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar rundunar sojin Amurka ta Afrika (US-AFRICOM) sun kashe akalla mayaƙan ƙungiyar ISWAP 21 a wani farmakin da suka kai a Jihar Borno.
An gudanar da farmakin ne a yankin Arege da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, bayan jami’an tsaro sun tattara bayanan sirri tare da gudanar da sa ido da ya tabbatar da taruwar mayaƙan ƙungiyar a yankin.
Masanin harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce majiyoyin tsaro sun tabbatar masa da nasarar farmakin.
A cewar rahoton, harin ya afkawa wani sansanin ISWAP da ake zargin mayaƙan ke amfani da shi wajen shirya hare-hare a yankin Tafkin Chadi da kewaye.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa farmakin ya yi nasarar hallaka mayaƙa da dama tare da raunana ƙarfin ƙungiyar wajen gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
“Harin da aka kai cikin ƙwarewa ya yi sanadin kashe ’yan ta’adda 21 tare da janyo babbar illa ga ayyukan ƙungiyar,” in ji wata majiya ta tsaro.
Rahoton ya ƙara da cewa farmakin wani ɓangare ne na ci gaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaƙi da ta’addanci da kuma rusa sansanonin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Haka kuma, majiyoyin sun ce an tsara aikin ne bisa sahihan bayanan sirri tare da aiwatar da shi cikin tsari domin kauce wa kura-kurai da kuma tabbatar da cimma manufar da aka sanya a gaba.
Farmakin na zuwa ne yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙara matsin lamba kan ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.