Rahotanni sun nuna cewa abokan hulɗar manyan kamfanonin sadarwa huɗu a Najeriya sun kashe kimanin Naira tiriliyan 9 wajen sayen kati da data a shekarar 2025, lamarin da ya ƙara wa kamfanonin kuɗaɗen shiga sosai.
Kamfanin MTN Nigeria ya samu kusan Naira tiriliyan 5.3 daga sayen kati da data da kwastomominsa miliyan 90.3 suka yi a shekarar da ta ƙare a ranar 31 ga Disamba, 2025. Hakan ya taimaka wa kamfanin sake komawa samun ribar haraji ta Naira tiriliyan 1.11.
Shi ma kamfanin Airtel Nigeria ya samu kusan Naira tiriliyan 3.1 daga kwastomominsa miliyan 60.9, yayin da yawaitar amfani da wayoyin zamani da intanet ke ci gaba da ƙaruwa a faɗin ƙasar.
Ko da yake kamfanonin Globacom da 9mobile ba su fitar da cikakken bayanan kuɗaɗensu a fili ba, masana sun kiyasta cewa kuɗin da suka samu daga sayar da kati da data sun kai kusan Naira tiriliyan 2 a shekarar 2025.
Rahoton ya bayyana cewa ƙaruwar kuɗin da mutane ke kashewa na da alaƙa da ƙarin farashin kuɗin kira da data, da kuma yawaitar amfani da intanet.
Bayanan MTN sun nuna cewa matsakaicin kuɗin da kowanne kwastoma ke kashewa a wata ya ƙaru daga dala 2.17 a 2024 zuwa dala 3.60 a 2025. Idan aka mayar da shi zuwa naira, hakan na nufin kowanne kwastoma yana kashe kusan Naira 5,184 duk wata.
Haka kuma, kamfanin ya bayyana cewa masu amfani da data sun ƙaru da kashi 11.6 cikin ɗari, yayin da amfani da wayoyin zamani ya ƙaru zuwa kashi 66.1.
Kamfanin Airtel ma ya ce matsakaicin kuɗin da kowanne kwastoma ke kashewa a wata ya ƙaru daga dala 1.7 zuwa dala 2.4 a shekarar 2025.
Hukumar NCC ta bayyana cewa ‘yan Najeriya yanzu suna amfani da kusan terabytes 45,800 na data a kowace rana, wanda ke nuna yadda amfani da intanet ke ƙaruwa sosai.
Sai dai duk da irin kuɗaɗen da mutane ke kashewa, masu amfani da layukan waya sun ci gaba da kokawa kan matsalar rashin ingancin sadarwa da matsalolin network a wasu wurare.
Masana sun ce ƙaruwar amfani da intanet, tashin farashin kuɗin kira da data, da kuma yawaitar amfani da wayoyin zamani ne suka haifar da wannan gagarumin kuɗin shiga da kamfanonin sadarwa suka samu.
Majalisar masu amfani da harkar sadarwa ta Najeriya ta buƙaci kamfanonin sadarwa su yi amfani da irin wannan kuɗaɗen wajen inganta ayyukansu da kuma samar da ingantacciyar sadarwa ga jama’a.