Sojoji huɗu sun jikkata bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai wa dakarun rundunar sojin Najeriya a kan hanyar Damboa Kumala Maiduguri da ke jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar 16 ga watan Mayu, kusa da mahadar Kumala a ƙaramar hukumar Konduga, yayin da dakarun runduna ta 25 ke gudanar da sintirin tabbatar da tsaro a yankin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin sun taka wani bam da aka binne a bakin hanya wanda ake sarrafawa daga nesa, kafin daga bisani maharan su bude musu wuta daga wurin kwanton ɓauna.
Duk da harin, dakarun sun mayar da martani tare da shiga musayar wuta da maharan domin dakile farmakin da kuma korar su daga yankin.
An tabbatar da cewa sojoji huɗu sun samu raunuka daban-daban a yayin artabun, sai dai babu rahoton rasa rai daga bangaren jami’an tsaron.
Bayan harin, rundunar sojin ta tura ƙarin dakaru zuwa yankin domin ƙarfafa tsaro da kuma ci gaba da gudanar da sintiri a hanyar.
Haka kuma, jami’an masu lalata bama-bamai sun isa wurin domin bincike da kawar da duk wasu abubuwan fashewa da ka iya ragewa a yankin.