Akalla jami’an ‘yan sanda 17 da ke halartar wani kwas na musamman kan yaki da ta’addanci sun rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne suka kai hari makarantar horas da rundunar musamman ta sojoji da ke Buni Yadi, a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar dare yayin da jami’an ke gudanar da horo a sansanin.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa sansanin daga bangarori daban-daban tare da bude wuta.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, ACP Anthony Placid, ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:15 na dare ranar 8 ga watan Mayu, inda jami’an suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasa.
Ya ce baya ga jami’an ‘yan sanda da suka mutu, wasu sojojin Najeriya ma sun rasa rayukansu yayin da suke mayar da martani kan harin, kodayake ba a bayyana adadin su ba.
Harin ya sake nuna yadda hare-haren ‘yan ta’adda ke ci gaba da barazana ga cibiyoyin tsaro a Arewa maso Gabas duk da kokarin hukumomi wajen dakile ayyukan Boko Haram da ISWAP.
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana jami’an da suka mutu a matsayin gwarazan kasa, yana mai jajantawa iyalansu tare da tabbatar da cewa sadaukarwar su ba za ta tafi a banza ba.
A nasa bangaren, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Yobe, Usman Jibrin, ya kai ziyarar jaje makarantar horaswar tare da gana wa da jami’an da suka tsira daga harin da shugabannin sojoji.
Ya kuma bukaci sauran jami’an da ke karbar horo su ci gaba da jajircewa domin cika burin abokan aikinsu da suka rasu.