Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiPDP za ta tantance Goodluck Jonathan gobe matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa...

PDP za ta tantance Goodluck Jonathan gobe matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027

Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki SAN ta shirya tantance tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan gobe Talata a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa shi kaɗai domin zaɓen shekarar 2027.

Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki SAN ta shirya tantance tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan gobe Talata a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa shi kaɗai domin zaɓen shekarar 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo, tsohon gwamnan jihar Plateau Jona Jang, da tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Tom Ikimi na cikin kwamitin mutum 14 da aka kafa domin tantance Jonathan.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Chief Olabode George, Babangida Aliyu, Maryam Ciroma, Zainab Maina, Josephine Anenih, Dr. Abdul Bulama, Dr. Esther Uduehi, shugaban PDP na Edo Tony Aziegbemi, Dr. Sunday Solarium, da Chief Anicho Okoro wanda zai kasance sakataren gudanarwa na kwamitin.

Sanarwar PDP ta ambaci cewa akwai ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya, kuma binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa Goodluck Jonathan ne kaɗai ya tsaya takarar.

A makon da ya gabata, sakataren yaɗa labarai na wannan ɓangaren PDP, Ini Ememobong, ya bayyana cewa Jonathan ya kammala sabon rajistar dijital ta jam’iyyar da INEC ta amince da ita.

Wannan ɓangaren PDP da ke samun goyon bayan gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kuma sanar da cewa zai tantance:

Yan takarar gwamna 112, na sanatoci 198, na majalisar wakilai 748 da kuma ƴan takarar majalisun jihohi 2,122.

Za a gudanar da tantancewar a faɗin ƙasa gobe Talata 19 ga Mayu, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.

Jam’iyyar ta ce fitar da sunayen kwamitocin tantancewa da kwamitocin sauraron ƙorafe-ƙorafe ya yi daidai da jadawalin shirye-shiryen zaɓen 2027.

A wani labarin daban, tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere, ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da nasarar PDP a mazabar sanatocin Owerri a zaɓen 2027.

Madumere ya ce yana da ƙarfi, gogewa da alaƙa ta siyasa da za su ba shi damar samun nasara tare da samar da ci gaba IIta hanyar ƙarfafa matasa da samar da ayyukan yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments