Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin raba kan jam’iyyun adawa ta hanyar farfado da jam’iyyar NDC.
Sakataren yaɗa labaran ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi ne ya yi wannan zargi yayin hira da jaridar The Sun.
Bolaji Abdullahi ya ce gwamnatin APC ƙarƙashin Tinubu ta jefa mutane cikin wahala da talauci saboda manufofin tattalin arziƙi da suka shafi rayuwar talakawa.
A cewarsa, akwai tsoro a tare da shugaban ƙasa saboda yadda yake kallon zaɓen 2027.
“Shugaban ƙasa mai 32% na karɓuwa a wurin jama’a shugaban ƙasa ne da za a iya kayarwa. Shi ya sa yake tsoro,” in ji shi.
Bolaji Abdullahi ya kuma ce yana da wahala ya tuna wani fanni da zai ce gwamnatin Tinubu ta yi abin a yaba.
“Bangaren lafiya? Rayuwar jama’a? Mutane masu mutunci sun koma mabarata a ƙarƙashin wannan gwamnati saboda manufofinta marasa kyau,” ya faɗa.
Ya soki yadda gwamnati ke kashe kuɗi wajen tafiye-tafiye yayin da ake roƙon talakawa su ƙara haƙuri da halin matsin rayuwa.
ADC ta kuma yi zargin cewa ana ƙoƙarin haddasa rikici a cikin jam’iyyar domin raunana haɗakar adawa kafin zaɓen 2027.
“Shi ya sa suke yin duk abin da za su yi domin tarwatsa ADC, har da ƙirƙirar NDC domin raba kan adawa,” in ji Bolaji Abdullahi.
Ya ƙara da cewa duk wanda ba ya goyon bayan haɗakar adawa yana aiki ne domin amfanin shugaban ƙasa.