Ƙungiyar Arewa Youth Assembly ta bayyana goyon bayanta ga shugaban ƙasa Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Ta bayyana cewa ya kamata mulki ya ci gaba da kasancewa a kudancin Najeriya har zuwa 2031 bisa tsarin karɓa-karɓar mulki.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi, kakakin ƙungiyar, Mohammed Sanni, ya zargi wasu gwamnoni da ƙoƙarin haddasa rikici a cikin jam’iyyar APC domin hana Tinubu yin wa’adi na biyu.
Kalaman nasa sun biyo bayan rahotannin da ke nuna akwai rabuwar kai a cikin PGF, inda ake zargin wasu gwamnoni na goyon bayan Hope Uzodimma, yayin da wasu ke mara wa Dapo Abiodun baya.Sanni ya ce bai kamata mulki ya koma Arewa kafin shekarar 2031 ba.
“Duk da mun yarda cewa kowa — ko gwamna ne, sanata ko ɗan ƙasa — yana da damar amfani da haƙƙinsa na dimokuraɗiyya, mun san abin da ka iya faruwa idan aka mayar da mulki Arewa a 2027 maimakon a bi tsarin karɓa-karɓar mulki wanda ya tanadi Kudu ta kammala wa’adinta zuwa 2031,” in ji shi.
Ya kuma yi zargin cewa masu adawa da Tinubu na son amfani da dandalin gwamnoni wajen raunana APC kafin zaɓen gaba.
“A cikin irin shirin da aka gani kafin zaɓen 2015, waɗannan maƙiyan Tinubu da Najeriya suna son amfani da PGF wajen kai hari ga dimokuraɗiyyarmu,” in ji Sanni.
Da yake tuna rikicin siyasar da ya faru kafin zaɓen 2015, ya ce:“Idan za ku tuna, matsalar da tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya fuskanta, wadda ta sa ya rasa mulki, ta fara ne daga rabuwar kai a cikin kungiyar gwamnoni ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Ribas, Rt Hon Rotimi Amaechi.”
Ya kuma buƙaci Abiodun da Peter Mbah su ba Tinubu, kungiyar gwamnoni, Uzodimma da APC haƙuri kan abin da ya kira “yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba”.
Sanni ya kuma roƙi majalisun dokokin jihohin Ogun da Enugu su fara shirin tsige gwamnonin biyu bisa zargin haddasa rikici a cikin APC.