Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya gobe Talata 05 ga watan Mayu 2026, a matsayin ranar da zai jagoranci rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan Kano Shawara kan harkokin yada labarai Ibrahim Adam ya fitar.
Idan za a iya tuna wa a makonnin da suka gabata Iconic Times24 ta ruwaito majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tare da amincewa gwamnan ya nada Murtala a matsayin mataimakin gwamnan domin maye gurbin Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya dauka da ƙansa.
Sanarwar ta ce za a gudanar da taron rantsuwar ne a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano da misalin karfe 11 na safe.
Tuni dai masoya da magoya bayan Garo suke ta yshirye-shirye domin gudanar da bukukuwa na Murnar zaman Murtala mataimakin gwamnan kano.
Masu nazari kan harkokin siyasa suna ganin nada Murtala Sule Garo a mukamin mataimakin gwamna zai taimaka wa gwamnatin Abba musamman ta fuskar siyasa.