Jam’iyyar ADC ta fitar da sabon jadawalin ayyuka na zaɓen fidda gwani na shekarar 2026, tare da rage kuɗin fom, bayan shawarwari da shugabannin jam’iyya, masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasa.
Bisa sabon jadawalin, za a fara sayar da fom daga ranar 1 zuwa 4 ga Mayu, 2026, yayin da saye da miƙa fom da aka cika za su gudana daga 6 zuwa 13 ga Mayu, inda ranar 13 ga Mayu ita ce ranar ƙarshe.
A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, za a gudanar da tantance ‘yan takara daga 14 zuwa 15 ga Mayu, yayin da za a fitar da sakamakon tantancewar ranar 17 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, za a saurari ƙorafe-ƙorafe daga 18 zuwa 19 ga Mayu, sannan a fitar da jerin sunayen waɗanda suka tsallake tantancewa ranar 20 ga Mayu, 2026.
Za a gudanar da zaɓen fidda gwani na majalisar jiha, majalisar wakilai da majalisar dattawa a ranar 21 ga Mayu, 2026, sai na gwamna a ranar 22 ga Mayu, 2026.
Zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gudana a ranar 23 ga Mayu, 2026. Bayan haka, za a yi taron kwamitin zartarwa na ƙasa NEC ranar 25 ga Mayu, sannan babban taron ƙasa a ranar 26 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, jam’iyyar ta rage kuɗin fom kamar haka:
Shugaban ƙasa – Naira miliyan 90
Gwamna – Naira miliyan 30
Majalisar dattawa – Naira miliyan 10
Majalisar wakilai – Naira miliyan 5
Majalisar jiha – Naira miliyan 2
Jam’iyyar ta kuma ci gaba da ba da rangwame kamar yadda aka saba:
Matasa daga shekaru 18–35, rangwamen kashi 50
Mata da masu nakasa – rangwamen kashi 25
A cewar Abdullahi, waɗannan sauye-sauye sun fito ne daga shawarwari masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin jam’iyya, sauƙaƙa shiga takara, da kuma tabbatar da cewa ADC ta kasance jam’iyya mai gaskiya da haɗa kowa a harkokin siyasa.