Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmurka ta janye dokar dakatar da bada biza ga likitocin Najeriya sakamakon...

Amurka ta janye dokar dakatar da bada biza ga likitocin Najeriya sakamakon karancin likitoci a kasar

Kasar Amurka ta janye wata doka da ta dakatar da bayar da biza ga likitocin da suka yi karatu a kasashen waje, lamarin da ya bai wa likitoci daga Najeriya da kusan wasu kasashe 38 damar ci gaba da gabatar da bukatunsu.

Rahoton jaridar The New York Times ya nuna cewa dokar da aka kafa a watan Janairu ta dakatar da yanke hukunci kan tsawaita biza, izinin aiki da kuma katin zama na dindindin ga ‘yan kasashen kusan 39 da ke karkashin dokar hana shiga Amurka.

Wannan mataki ya hana likitoci da dama da suka yi karatu a kasashen waje damar gudanar da aikinsu.

Sai dai yanzu Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (US Citizenship and Immigration Services) ta sabunta ka’idojinta, inda ta ware likitocin lafiya daga cikin dokar dakatarwar, lamarin da zai ba da damar ci gaba da nazarin bukatunsu.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, “Bukatun da suka shafi likitocin lafiya za su ci gaba da samun kulawa.”

Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke fuskantar karancin ma’aikatan lafiya, inda hukumomi ke kiyasin cewa akwai gibi na likitoci kusan 65,000, kuma ana sa ran wannan gibi zai kara fadada a nan gaba.

Likitocin da suka yi karatu a kasashen waje na samar da kusan kashi daya cikin hudu na ma’aikatan lafiya a Amurka, inda da dama daga cikinsu ke aiki a bangaren kula da marasa lafiya na farko, musamman a yankunan karkara da wuraren da ba su da isassun ayyukan lafiya.

Dakatarwar bizar da aka yi a baya ta tilasta wasu likitoci zama ba tare da aiki ba, yayin da wasu kuma suka fuskanci yiwuwar rasa ayyukansu sakamakon jinkirin amincewa da takardunsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments