Mahukuntan Jamhuriya Nijar sun buƙaci a riƙa garƙame Masallatai da makarantun allo da zaran an kammala sallolin farilla, da dauƙar darasi domin hana baƙi sauka a ciki.
Gwamanti ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kauda duk wata bazanar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
A cikin wata wasika da ministan kula da harkokin cikin gidan Nijar, Janar Mohamed Toumba, ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 30,Afrilu,2026, ya aike wa gwamnonin jihohi da shugabannin gundumomi da na ƙananan hukumomi gwamnatin, ta umurcesu da su hana duk wata baƙuwar fuska kwanciya a Masallatai da kuma marakantun allo.
Haka ma gwamnatin ta buƙaci jama’a da su fallasa duk wani mutum da basu yarda dashi ba ga sarakan gargajiya da wakilan al’ummar yankunansu.
Gwamnatin ta ce daukar matakin ya zama dole lura da yadda makiyan ƙasar suka ɓullo da sabbin dabarun sajewa a cikin al’umma, domin tafka aika-aika.
Matakin gwamnatin sojin Nijar na zuwa ne ƙasa da kwanaki goma, bayan munanan hare-haren da haɗakar ƙungiyar mayaƙan Abzinawa ta FLA da takwarorinsu na ƙungiyar JNIM, suka ƙaddamar ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata a birane da dama na Bamako, tare da hallaka ministan tsaron ƙasar Sadio Camara.