Ƙasar Iran ta bayyana cewa har yanzu ba ta yanke shawara ba kan ko za ta halarci wani sabon zagaye na tattaunawar sulhu da Amurka ba, yayin da tawagar Amurka ta baro ƙasar domin zuwa Pakistan a ranar Litinin.
Rashin tabbas kan tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin da ya addabi yankin da kuma girgiza tattalin arzikin duniya ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi nuni da cewa zai iya ci gaba da kai hare-hare idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙare ba tare da cimma sulhu ba.
Tun bayan tattaunawar farko da aka yi a Islamabad wadda ta ƙare ba tare da yarjejeniya ba a farkon wannan wata, ɓangarorin biyu na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce har yanzu ba su da wani shiri kan sabon zagayen tattaunawar, kuma ba a yanke hukunci ba kan hakan.
Ya kuma zargi Amurka da aikata abubuwan da ba su nuna gaskiya wajen neman sulhu ba, inda ya ambaci toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran da kuma kwace wani jirgi a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
A nata ɓangaren Amurka, Trump ya zargi Iran da keta yarjejeniyar ta hanyar takura wa jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hormuz, wacce ke da muhimmanci ga kasuwancin duniya, kuma Iran ta kusan rufe ta gaba ɗaya.Rahotanni sun nuna cewa tawagar Amurka za ta nufi Pakistan nan ba da jimawa ba, yayin da Trump ya ce Iran ya kamata ta halarci tattaunawar, domin an riga an amince da hakan.
Ya kuma yi gargadin cewa idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙare ba tare da cimma yarjejeniya ba, to rikicin na iya ƙara tsananta.A sakamakon wannan rashin tabbas, farashin mai ya tashi sosai a ranar Litinin, bayan da Iran ta sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a kasuwannin duniya.