Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar tace fina-finai ta Kano ta rufe shagon saida magani saboda amfani...

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta rufe shagon saida magani saboda amfani da kalaman da basu dace ba

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta rufe wani shagon maganin gargajiya bayan zargin cewa mai shagon ya yi amfani da yara wajen tallata magungunan ƙara ƙarfin jima’i ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta rufe wani shagon maganin gargajiya bayan zargin cewa mai shagon ya yi amfani da yara wajen tallata magungunan ƙara ƙarfin jima’i ta hanyar da ba ta dace ba.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, an ce an ɗauki matakin ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama kan tallan, wanda ya ƙunshi kalamai da hotuna marasa dacewa.

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya tabbatar da cewa an rufe shagon tare da umartar mai sayar da maganin, wanda aka fi sani da Nagwale, da ya gurfana a gaban hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin.

Da yake magana kan lamarin, Daraktan sashen kula da ɗabi’a, Alhaji Zakari Garun Babba, ya bayyana cewa tallata irin waɗannan kayayyaki a bainar jama’a, musamman ta hanyar amfani da yara, babban laifi ne a ƙarƙashin doka.

Ya yi gargadin cewa irin wannan hali na iya jawo hukunci mai tsanani.“Masu sayarwa da masu tallata irin waɗannan kayayyaki dole su fahimci cewa amfani da yara ko abubuwan da ba su dace ba a tallace-tallace abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma yana da hukunci,” in ji shi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wanda ake zargi ya amsa laifinsa tare da neman gafarar al’ummar Kano.A matsayin wani ɓangare na ladabtarwa, hukumar ta umurce shi da ya bayar da gafara a rubuce, da murya, da kuma bidiyo, wanda za a ajiye a matsayin hujja a nan gaba.

Hukumar ta kuma jaddada cewa tana da ikon doka na sa ido kan ayyukan masu maganin gargajiya, musamman a bangaren talla, domin tabbatar da bin ƙa’idojin ɗabi’a.Ta kuma tabbatar da ƙudirin ta na kare ɗabi’ar al’umma da kuma kare yara daga cin zarafi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments