Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMatasa sun bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 kan manyan ayyuka a...

Matasa sun bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 kan manyan ayyuka a Arewa

Matasan Arewa sun ce bai dace a mayar da ci gaban yankin alkawarin siyasa kawai ba

Kungiyar matasan Arewa (NYA) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 da ta fito da cikakken bayani mai gamsarwa kan halin da ake ciki na tashar tsandauri na Dala da ke Kano da kuma aikin bunƙasa Kolmani da ke jihohin Bauchi da Gombe.

A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a madadin matasa daga jihohi 19 na Arewa, kungiyar ta nuna damuwa kan abin da ta kira jinkiri mai tsawo, rashin tabbas da kuma rashin gaskiya da ke tattare da wadannan manyan ayyukan tattalin arziki guda biyu.

NYA ta bayyana cewa tun da farko an gabatar da wadannan ayyuka a matsayin manyan tsare-tsare da za su kawo sauyi, su bunkasa masana’antu, su kara kasuwanci tare da inganta harkokin makamashi a yankin. Sai dai ta koka cewa da alama ayyukan sun tsaya cak, lamarin da ke jefa masu ruwa da tsaki cikin shakku.

Da take magana kan tashar Dala, kungiyar ta ce duk da cewa an taba ayyana cewa har yanzu ba ta fara aiki yadda ya kamata ba. Ta ce maimakon rage kudin jigilar kaya da samar da ayyukan yi, tashar na ci gaba da zama ba a amfani da ita yadda ya dace.

Saboda haka, kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar fayyace halin da aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna yake ciki, tana mai cewa wannan aiki na da matuƙar muhimmanci ga nasarar tashar. Haka kuma ta nemi a bayyana duk wasu matsalolin doka, na gudanarwa ko na mallaka da ke hana tashar yin aiki yadda ya kamata.

Dangane da aikin hakar mai na Kolmani, NYA ta tuna cewa kaddamar da aikin ya haifar da farin ciki da fata a yankin, musamman kasancewarsa wani muhimmin mataki na fara hako mai a Arewacin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments