Matar jagoran Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, wato Zeenatuddeen Zakzaky, ta yi kira ga Musulmi da Kiristoci a duniya da su haɗa kai domin yaƙi da zalunci da kuma tabbatar da adalci a duniya.
Ta bayyana hakan ne a wani taron kasa da kasa na Musulunci da aka gudanar a jihar Bauchi, inda ta jaddada cewa dole ne mutane su tsaya tsayin daka wajen yakar zalunci, domin ba za a samu zaman lafiya da ci gaba ba idan aka yi shiru ana kallon rashin adalci.
Ta kuma ce wajibi ne Musulmi su rayu bisa koyarwar Alƙur’ani da koyarwar Annabi, tare da nuna cewa manufar taron ita ce tunatar da mutane hakkinsu na rayuwa cikin gaskiya da adalci.
Dangane da rikice-rikicen duniya, musamman wanda ya shafi Amurka, Isra’ila da Iran, ta bayyana cewa lamarin yana kama da gwagwarmayar masu zalunci da waɗanda ake zalunta, inda ta bukaci mutane su kasance a bangaren gaskiya da adalci.
Ta kuma jaddada cewa Musulmi da Kiristoci dole ne su haɗa kai wajen yaƙi da zalunci a ko’ina cikin duniya, tana mai cewa yin shiru a gaban zalunci yana kara dagula al’amura maimakon gyara su.
Ta kuma bukaci mutane su kasance masu himma wajen kare hakkokin bil’adama da kuma nuna goyon baya ga waɗanda ake zalunta, musamman a yankunan da ake fama da rikice-rikice.