Shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar a sake komawa kan tattaunawar sulhu tsakaninsa da Iran cikin wannan mako, duk da ya dage kan cewa babu abinda zai sanya shi sauka daga kan buƙatun da ya miƙawa Iran guda 15 tun da fari.
Yayin da yake tattaunawa da kafar New York Post, Trump ya ce sabuwar tattaunawar da za’a shiga ba zata ƙunshi shawarar da mataimakinsa JD Vance ya bashi kan janyewa Iran takunkumin sarrafa makamashin Uranium na tsahon shekaru 20 ba.
Ya ƙara tabbatar da yiwuwar tattaunawar a wannan mako, shugaban ya shawarci ƴan Jarida da masu sanya Idanu da suka halarci zaman wancan mako na birnin Islamabad da kada su koma ƙasashen su.
Wani abu da ya ɗauki hankali yayin tattaunawar shine yadda shugaban ya ƙi ayyana mataimakinsa JD Vance a matsayin wanda zai jagoranci Amurka yayin wannan tattaunawa.
Ko da aka tambaye shi kan sake nazari game da shawarar mataimakinsa na ɗagewa Iran takunkumin sarrafa Uranium na tsahon shekaru 20 Trump ya ce tun kafin fara yaƙin, babbar manufar itace haramtawa Iran kera makamin Nuclear, a don haka idan har aka basu waccan dama zasu fara tsammanin sun yi nasara ne, kuma shi sam abinda baya buƙata kenan.
Duk da ya chachaki mahukuntan Iran da ƙin bayar da haɗin kai domin samun matsaya a wancan zama, amma ya nuna ƙwarin gwiwar cewa wannan sabon zama da za’a yi cikin kwanaki biyu masu zuwa zai haifar da ɗa mai ido.