Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin Najeriya sun kai samame kan sansanin ‘yan ta’addan IPOB

Sojojin Najeriya sun kai samame kan sansanin ‘yan ta’addan IPOB

Dakarun tsaron Najeriya sun afka wa sansanin mayakan Indigenous IPOB

Dakarun sojin Najeriya sun kai samame a sansanin ‘yanta’addan IPOB’ESN a faɗin kudu maso gabashin ƙasar inda suka lalata maɓoyar tare da ƙwace makamai.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X ranar 15 ga watan Afrilu ta ce wani samame da dakarun runduna ta musamman ta Operation Eastern Sanity suka kai dajin Ajali, a ƙaramar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu ranar 14 ga watan Afrilu ya tilasta wa ‘yanta’addan IPOB/ESN tserewa inda suka bar kayayyakinsu ciki har da nakiyar tarwatsa tankokin yaƙi.

“Tawagar jami’an tsaro ta kawar da abubuwa masu fashewa da ta samu a wurin, inda ta hana yiwuwar yin lahani ga dakaru da fararen-hula,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa dakarun sun lalata sansanonin da mayaƙan ke ɓuya ta yadda ba za su iya sake haɗuwa a wuraren ko kuma su samu wata kariya a wuraren ba.

A wani samame makamancin hakan a ranar Talatan, dakarun da aka tura Adani a ƙaramar hukumar Uzo-Uwani, da suke aiki bisa bayanan sirrin da suka samu daga jami’an tsaro na farin kaya DSS, sun bi sawu tare da kama wani kuɗin fansa da ke da alaƙa da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments