Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati za ta ƙarfafa sojoji domin kawo ƙarshen rashin tsaro – Tinubu

Gwamnati za ta ƙarfafa sojoji domin kawo ƙarshen rashin tsaro – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa rundunar sojin Najeriya domin yaƙar ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a fadin ƙasar.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa rundunar sojin Najeriya domin yaƙar ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a fadin ƙasar.

Da yake jawabi yayin ziyarar yini guda a Jihar Bayelsa, inda ya ƙaddamar da muhimman ayyuka da Gwamna Douye Diri ya aiwatar, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da horaswa da samar da kayan aiki ga sojoji domin tinkarar matsalolin tsaro.

Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murƙushe ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan tare da matarsa Patience Jonathan sun halarci taron.

Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar akwai tashar samar da lantarki mai ƙarfin megawatt 60 a Elebele, gadar Angiama-Oporoma mai tsawon mita 630, da kuma gyaran hanyar birnin Yenagoa da ke haɗa Airport Road zuwa Sagbama-Ekeremor Road.

Bayan kaddamar da ayyukan, Tinubu ya yabawa gwamnatin jihar kan ci gaban da ta kawo, yana mai cewa irin wadannan ayyuka na samar da ayyukan yi da fata ga al’umma.

Ya kuma jaddada cewa haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ci gaba.

Tinubu ya bayyana tashar wutar lantarkin a matsayin muhimmin mataki na bunkasa masana’antu, tare da tabbatar da cewa za a inganta samar da wutar lantarki domin tallafa wa tattalin arziki.

A nasa bangaren, Gwamna Douye Diri ya ce manufofin gwamnatinsa sun kawo sauye-sauye musamman a bangaren wutar lantarki, inda aka kafa tashar wuta domin samar da ingantaccen haske ga jama’a.

Ya kara da cewa gadar Angiama-Oporoma da aka dade ana watsi da ita yanzu an kammala ta, lamarin da zai taimaka wajen bunkasa yankunan mai.

Haka kuma, ya ce hanyar Yenagoa-Oporoma za ta haɗa sama da al’ummomi 60, ta rage lokacin tafiya da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments