Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dinkin Duniya ta miƙa bukata ga Amurka da Iran kan zaman...

Majalisar Dinkin Duniya ta miƙa bukata ga Amurka da Iran kan zaman sulhu

MDD ta jaddada muhimmancin tattaunawa mai ma’ana tsakanin Amurka da Iran.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da tattaunawar zaman lafiya da Amurka da Iran suka amince za su yi, inda ya buƙaci ɓangarorin biyu su shiga tattaunawa da ”zuciya ɗaya”.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, kakakin Gutteres, Stephane Dujarric ya ce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya yi kira ga duka ɓangarorin biyu su yi amfani da damar tattaunawar wajen kawo ƙarshen rikicin ta hanyar amincewa da cikakkiyar yarjejeniyar.

“Babban sakataren ya jaddada cewa babu wata hanyar kawo ƙarshen yaƙin cikin zaman lafiya da ta wuce hanyar diplomasiyya,” cewar Dujarric.

Jakadan Guterres na musamman ya isa yankin domin tallafa wa yunƙurin diplomasiyyar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments