INEC ta bayyana cewa ta yi rijistar sama da mutane miliyan 3.4 a mataki na biyu na ci gaba da rijistar masu kada kuri’a a fadin Najeriya.
A cewar rahoton mako na 13 da hukumar ta fitar a Abuja, an kammala rijistar mutane 3,441,121 zuwa ranar 3 ga Afrilu, wanda ya hada da wadanda suka yi rijista ta yanar gizo da kuma wadanda suka je cibiyoyi kai tsaye.
INEC ta ce mutane 2,068,384 sun kammala rijista ta yanar gizo, yayin da wasu 1,372,737 suka yi rijista a wuraren da aka tanada a fadin kasar.
Dangane da jihohi, Jihar Jigawa ce ta fi yawan masu rijista da mutum 201,047, wato kashi 5.84, sai Lagos da 181,095, yayin da Kano ta zo ta uku da 177,681.
Matasa sun fi yawa a cikin wadanda suka yi rijista, inda masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 suka kai 2,354,768, wanda ya kai kashi 68.43 na jimillar.
A bangaren jinsi kuwa, mata sun fi yawa da mutum 1,922,143, 55.86 cikin dari na adadin, yayin da maza suka kai 1,518,978, kashi 44.14.
Dangane da sana’o’i, dalibai su ne mafi yawa da mutum 1,235,931 sai ‘yan kasuwa da 701,912, sannan manoma da masunta da 615,967.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 48,330 masu nakasa sun yi rijista a wannan lokaci.
INEC ta ce wadannan alkaluma na wucin gadi ne, saboda za a sake tantance bayanan kafin a kammala su, tare da amfani da tsarin tantance bayanan yatsu.
Haka kuma, an dakatar da rijistar masu kada kuri’a a Abuja bisa tanadin dokar zabe ta 2022, bayan gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 21 ga Fabrairu.
A karshe, INEC ta bukaci ‘yan Najeriya da suka cancanta amma ba su yi rijista ba da su gaggauta yin hakan kafin wa’adin ya cika.