Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutum 11 tare da kone gidaje sama da 50 a wani rikicin kabilanci da ya faru ranar Juma’a a yankunan Akyawa da Udege Kasa da ke karamar hukumar Nasarawa.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Lafia.
Ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a lokacin da wasu da ake zargi ‘yan daba ne suka kai harin ramuwar gayya bayan zargin kashe wasu ‘yan uwansu biyu.
A cewarsa, “a yayin harin, an kashe mutum 11, yayin da aka kona gidaje kusan 52 a cikin al’ummomin biyu.”
Nansel ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Shetima Mohammed, ya jagoranci wata tawaga zuwa wuraren da lamarin ya faru domin tantance irin barnar da aka yi da kuma tabbatar da dawo da zaman lafiya.
Ya ce kwamishinan ya nuna matukar alhini kan wannan lamari mai tayar da hankali, tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu da al’ummomin da abin ya shafa.
Haka kuma ya ba su tabbacin cewa rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da an yi adalci.
A cewarsa, kwamishinan ya bayar da umarnin fara farautar wadanda suka aikata wannan danyen aiki, inda ya umarci rundunonin musamman da bangaren bincike su gaggauta gano su, kama su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.