Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSakataren APC na ƙasa ya bukaci INEC ta soke rajistar ADC

Sakataren APC na ƙasa ya bukaci INEC ta soke rajistar ADC

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya bukaci INEC da ta soke rajistar jam’iyyar ADC.

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya bukaci INEC da ta soke rajistar jam’iyyar ADC.

Ya bayyana cewa rikicin shugabanci da ke addabar ADC ya samo asali ne daga matsalolin cikin gida da kuma rashin bin ka’idojin doka, ba wai daga wani tsoma bakin gwamnati ba.

Basiru ya kuma karyata zargin da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kokarin kafa jam’iyya guda a kasar, yana mai cewa shugaban kasa ba shi da ikon soke rajistar kowace jam’iyya ko tsoma baki cikin harkokin INEC.

Ya kara da cewa matakin da INEC ta dauka kan rikicin ADC ya biyo bayan hukuncin kotu ne, inda aka umarci bangarorin jam’iyyar da su tsaya a yadda suke har sai an kammala shari’ar.

APC ta kuma zargi bangaren ADC da ke ƙarƙashin jagorancin David Mark da kin mutunta doka, musamman yadda suke kokarin ci gaba da gudanar da taruka duk da cewa akwai shari’a a gaban kotu.

Basiru ya shawarci ADC da ta magance rikicin cikin gida maimakon zargin wasu, yana mai cewa duk wani sakamako da zai biyo baya daga rashin bin doka ba za a dora shi kan APC ko gwamnati ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments