Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya sadaukar da duk albashinsa domin tallafa wa sojojin Najeriya

Tinubu ya sadaukar da duk albashinsa domin tallafa wa sojojin Najeriya

Tinubu ya bada gudummawar albashinsa ga sojojin Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da bayar da dukkan albashinsa ga sojojin da suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan wadanda suka rasu.

Haka kuma, ya kafa wani asusun tallafi na musamman domin kula da irin wadannan mutane.

Shugaban ya bayyana wannan shiri ne a ranar Lahadi yayin bikin cika shekaru 74 da haihuwarsa, domin girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar sojojin kasar nan.

Ya umarci Akanta Janar na Tarayya da ya bude wani asusu na musamman domin wannan shirin, wanda zai tallafa wa sojojin da suka jikkata da kuma zawarawa, mazajen da suka rasa matansu, da ‘ya’yan wadanda suka rasu suna yi wa kasa hidima.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments