Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan bindiga sun shiga wani asibiti tare da yin awon gaba da...

Yan bindiga sun shiga wani asibiti tare da yin awon gaba da ma’aikatan lafiya

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun shiga asibiti tare da sace ma’aikata.

Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani asibiti a jihar Ondo.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a wani asibiti da ke yankin Oke Ijebu a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan waɗanda suka kawo harin da misalin ƙarfe 2:00 na dare, sun yi awon gaba da dukkan ma’aikatan da ke bakin aiki.

Wani mara lafiya a asibitin ya ce maharan sun zo ne da wata babbar motar bas, inda suka shiga asibitin da ke kusa da makarantar Mega School, suka kwashe ma’aikatan lafiya shida, har da wasu ɗalibai masu neman ƙwarewa.

Sai dai kuma, jami’an hukumar tsaro ta jihar Ondo, wadda aka fi sani da Amotekun, sun ceto mutane biyar a wasu samame biyu daban-daban da suka kai a daren jiya a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar.

Kwamandan rundunar, Akogun Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an sace wani mutum ɗan shekara 45 da ɗansa ɗan shekara 15 a Pelebe, da ke bayan garin hanyar Oda-Akure, tsakanin ƙarfe 7:30 na yamma zuwa 8:00 na dare.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments