Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa ’yan sandan jihohi za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro a Najeriya.
Ministan kula da harkoki yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ƙarbi bakuncin kwamitin kafa yan sandan jihohi na babban sifeton yan sandan Najeriya.
Ya ce kudurin ya zo daidai da kudurin sabunta fata na gwamnatin Tinubu, tare da fadada aikin ɗan sanda domin bawa jihohi dama wanda zai inganta tsarin aikin da yaƙi da matsalolin tsaro.
Ministan ya ce yanayin tsaron da ake ciki a kasar nan na bukatar daukar sabbin matakai, saboda haka ya zama wajibi a kafa yan sandan na jihohi.