Kotun tarayya da ke jihar Jigawa ta dage hukunci a shari’ar Walida Abdulhadi, yarinya da ake zargin jami’in DSS ya sace kuma ya yi mata fyade, zuwa ranar 28 ga Afrilu, 2026.
A baya, kotu ta riga ta dage sauraron shari’ar ranar 11 ga Maris don ba wa lauyan kare wanda ake tuhuma damar shirya takardun kare kansa a kan zargin Walida, ’yar ƙaramar hukumar Hadejia, da ya ɗauke a shekarar 2023.
A zaman kotu da aka yi ta Zoom, lauya Abdulmalik Sani ya roki karin lokaci don shigar da takardun kare kansa, yana mai cewa suna bukatar karin bayanai.
Sai dai lauya mai gabatar da kara, Kabir Adamu, ya bayyana cewa sun shirya tsaf kuma ya kalubalanci bukatar karin lokaci.
Mai shari’a, Justice Hassan Dikko, ya dage shari’ar zuwa 28 ga Afrilu domin yanke hukunci.