Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Sokoto na shirin sabunta fadodin hakimai a fadin jihar

Gwamnatin Sokoto na shirin sabunta fadodin hakimai a fadin jihar

Ahmed Aliyu ya ɗauki matakin farfaɗo da fadodin hakimai a dukkanin ƙananan hukumomin Sokoto.

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara gyaran fadodin hakimai a fadin jihar domin inganta harkokin shugabancin gargajiya.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Malam Abubakar Bawa, ya fitar.

Gwamnan bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, a lokacin gaisuwar Sallah.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri na da nufin tabbatar da cewa hakimai, waɗanda su ne mafi kusa da al’umma a matakin ƙasa, suna da ingantattun muhallai da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya ce, “Ba mu manta da halin da wasu daga cikin fadodin hakimai ke ciki ba, inda da dama daga cikinsu suka lalace.

Nan ba da jimawa ba za mu fara aikin gyaransu, inda za mu fara da fadar Hakimin Wurno.”

Haka kuma, gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafada da kafada da Majalisar Masarautar Sokoto domin shawo kan matsalolin da ke addabar al’umma, musamman batun tsaro a yankunan karkara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments