Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya yi amfani da bidiyo a shafin sa wajen sukar shugaban...

Trump ya yi amfani da bidiyo a shafin sa wajen sukar shugaban Birtaniya Starmer.

Donald Trump, shugaban Amurka, ya sake tayar da cece-kuce bayan wallafa wani bidiyo a shafinsa na Truth Social da ke yi wa Firaministan Ingila, Keir Starmer, ba’a.

Bidiyon, wanda aka samo daga wani shirin barkwanci na talabijin, ya nuna Starmer a matsayin wanda ba shi da ƙarfi wajen yanke hukunci, musamman a wani yanayi da ya shafi hulɗarsa da Trump.

A cikin shirin, an nuna Firaministan yana kaucewa amsa kiran waya daga Trump, abin da ke nuna kamar yana jin tsoron yadda zai mayar da martani. Ko da yake Trump bai yi ƙarin bayani ba kan bidiyon, ana ganin hakan wata hanya ce ta sukar Starmer, musamman kan matsayinsa a wasu batutuwan siyasa.

Masu sharhi na ganin wannan mataki na iya ƙara dagula dangantakar siyasa tsakanin Amurka da Birtaniya, a daidai lokacin da hulɗar shugabannin biyu ke fuskantar ƙalubale.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments