Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta bari matsalar tsaro ta rinjayi ƙoƙarin da take yi wajen ci gaban ƙasa ba, yana mai tabbatar da cewa za su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a faɗin Najeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da gwamnoni 23 a gidansa da ke Lagos domin bikin Sallah. Ya ce tsaro da walwalar al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke bai wa muhimmanci.
Ya ƙara da cewa ya tattauna da shugabannin ƙasashen waje, ciki har da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, kan yadda za su taimaka wa Najeriya da kayan aiki da goyon baya domin ƙarfafa tsaro. Haka kuma, ya ce yana ci gaba da neman haɗin gwiwa daga sauran ƙasashe.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa rashin tsaro babbar barazana ce ga ci gaba da bunƙasar ƙasa, don haka ya buƙaci gwamnoni da su haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen yaƙar masu aikata laifi.
Ya kuma yi gargadin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya ƙara hauhawar farashin kayayyaki da rage ƙarfin sayen jama’a, inda ya buƙaci a ɗauki matakan rage tasirin hakan ga talakawa.
Tinubu ya shawarci gwamnoni da su ƙirƙiri manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar jama’a tare da rage tasirin hauhawar farashi, musamman a fannin makamashi da sufuri.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya gode wa shugaban ƙasa kan ƙoƙarinsa da kuma ziyarar da ya kai Birtaniya, yana mai cewa hakan ya ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnoni na ci gaba da tattaunawa kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, inda za su miƙa takarda ga majalisar dokoki domin samar da tsarin doka a kai.