Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMutane sama da 69 sun rasu sakamakon wani hari a asibitin Sudan

Mutane sama da 69 sun rasu sakamakon wani hari a asibitin Sudan

Akalla mutum 69 sun mutu wasu 89 kuma sun jikkata sakamakon wani harin da aka kai kan wani asibiti a yankin Darfour da ke kudancin  Sudan da yammacin jiya Asabar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban hukumar lafiya ta duniya,Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar kaduwa game da harin da aka kai asibitin koyarwa  ta El-Daein da ke Kudancin Sudan inda mutum sama 60 da suka hada da yara kanana 13 suka rasa rayukansu.

Rikicin da ya hada tsoffin aminan juna a Sudan tun daga shekara 2023, ya kazanta bayan da bangarorin biyu suka fara amfani da jirage marasa matuka domin kai hare-hare kan gine-gine jama’a da makarantu da kuma asibitoci.

Yankin El-Daein da ke karkashin ikon mayakan RSF ya na fuskantar hare-hare kai-a-kai  daga dakarun gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments