Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Tukur Buratai, ya bayyana cewa bai kamata a ɗora masa alhakin rashin bayyana sunayen mutanen da ake zargi da tallafa wa ta’addanci a ƙasar ba. Sai dai ya ce an san waɗannan masu ɗaukar nauyin ta’addanci, kuma suna cikin al’umma.
Da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Juma’a, tsohon Laftanar Janar ɗin ya ce hukumomin da suka dace sun san waɗanda ke bayan tallafin, amma suna da dalilansu na rashin bayyana sunayen a bainar jama’a.Ya ce: “ Ba za a ce ni ne zan ɗauki alhakin bayyana sunayen masu tallafa wa ta’addanci ba. Ba wai kawai ambaton sunaye ba ne; hukumomin sun san dalilin da ya sa ba a fitar da su ba. Abin da ya dace shi ne a ɗauki mataki.
Waɗannan mutanen suna cikin al’umma har yanzu, kuma an san su. Ni ina ɗaukar alhakin abubuwan da suka shafi rundunar soji kaɗai. ”Buratai ya kuma bayyana cewa shawarar sake tarbiyyar waɗanda suka tuba daga Boko Haram ba ta fito daga sojoji ba, sai dai daga gwamnati.
Ya ƙara da cewa: “A farko, mun ba su wa’adin miƙa wuya a shekarar 2016, kuma idan suka miƙa wuya, muna ba su damar wucewa lafiya sannan mu miƙa su ga hukumomin da suka dace domin a sake tarbiyyar su.”
Tsohon jakadan ya kuma nuna damuwa kan matsalolin tsaro a ƙasar, inda ya buƙaci a ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri domin yaƙi da ta’addanci da makamantansu. Haka kuma, ya buƙaci gwamnati ta ƙara ɗaukar sabbin jami’an tsaro domin inganta tsaro a faɗin ƙasar.
Kiran a bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci ya daɗe yana ci gaba, musamman bayan da gwamnatin tarayya ta sha alƙawarin cewa za ta fallasa tare da gurfanar da masu tallafa wa ‘yan ta’adda.
A shekarar 2021, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta gano wasu mutane da ƙungiyoyi da ake zargi da tallafa wa ta’addanci, wanda hakan ya sa jama’a suka yi tsammanin za a bayyana sunayensu.Haka kuma, Hukumar NFIU ta taɓa bayyana cewa ta gano wasu mu’amalolin kuɗi masu alaƙa da ta’addanci, yayin da hukumomin tsaro suka ƙara bincike kan hanyoyin da ake bi wajen tallafa wa ‘yan ta’adda.
Duk da waɗannan bayanai, har yanzu ba a bayyana sunayen waɗanda ake zargi ba, abin da ke jawo suka daga ƙungiyoyin fararen hula da masana tsaro, waɗanda ke cewa buɗaɗɗen bayani yana da muhimmanci wajen kawo ƙarshen rashin hukunci.
Najeriya dai ta shafe sama da shekaru goma tana fama da matsalar ta’addanci a Arewa maso Gabas, inda Boko Haram da rabe-rabenta suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba mutane da dama da muhallansu.