Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroSojoji sun kama masu kai kayan aiki ga ‘yan ta’adda a Kwara

Sojoji sun kama masu kai kayan aiki ga ‘yan ta’adda a Kwara

Sojoji sun cafke mutum uku da ake zargi da shirin kai babura ga ‘yan ta’adda

Sojojin rundunar ‘Operation Savannah Shield’ sun kama wasu mutum uku da ake zargi da kai kayan tallafi ga ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama mutanen ne da misalin 7.35 na safe a ranar 15 ga watan Maris, 2026 a lokacin da sojoji ke bakin aiki a wani sansanin su na yankin Kaiama.

A cewar majiyoyin, da fari sojojin sun kama wani mutum guda da ake zargi yana shirin kai wa ‘yan ta’adda babura guda uku domin amfani da su.

Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga kama wasu mutum biyu, waɗanda ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP/Boko Haram ne, kuma an ce sun iso Kaiama ne domin karɓar baburan.

Rahotannin da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X sun nuna cewa waɗannan mutanen na shirin kai baburan ne zuwa ga ‘yan ta’adda da ke aiki a ƙauyen Nuku.

A halin yanzu, ana tsare da waɗanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike a kansu domin gano cikakken bayani kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments