Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane biyar ‘yan asalin Burkina Faso da ke aiki a wani wurin hakar zinare kusa da kauyen Arafa a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 11:15 na safe a ranar 14 ga Maris, 2026, lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye wurin hakar ma’adinan tare da tafiya da ma’aikatan zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.