Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa sojojin kasar nan sun kashe ƴan bindiga 45 da suka kai hari wani ƙauye a jihar Katsina.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Katsina, Hon. Nasiru Mu’azu ya bayyana cewa, cikin ƴan bindigar da aka kashe har da wasu manyan kwamadandojin ƴan bindiga biyu da suka gawurta suka addabi wasu yankunan jihohin Katsina da Zamfara, wato Kacalla Alti da Kacalla Damale waɗanda suka kasan ce ‘yan’uwan juna ne.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da maraice kamar yadda hukumomin jihar suka tabbatar.
Rahotonni sun ce tun da farko ƴan bindigar waɗanda suka taso daga jihar Zamfara mai makwabtaka da Katsina, sun kai hari ƙauyen Alhazawa na ƙaramar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu.
Toh sai dai mazauna garin sun nuna turjiya da jarumta inda suka kashe huɗu daga cikin maharan.
Kwana daya bayan hakan ne kuma ƴanbindiga suka sake taruwa da nufin ɗaukar fansa kan mazauna ƙauyen, inda suka ci karo da sojoji a kan hanyar tasu, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin su.
Bayanai sun nuna cewa sojoji uku ne suka rasa rayukan su lokacin gumurzun.