Mayaƙan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojin Najeriya a garin Ngoshe, da ke ƙaramar hukumar Gwoza , inda suka kashe aƙalla sojoji tara da kuma wani limamin gari, kamar yadda majiyoyin soji uku suka bayyana da yammacin Laraba.
‘Yanta’addan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 14 a hare-hare biyu
‘Yan ta’addan dai ISWAP sun kashe sojojin 14 tare da jikkata wasu a hare-hare da suka kai sansanonin soji biyu a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar Talata da daddare, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Hakan na faruwa ne yayin da ‘yan bindigar ke zafafa kai hare-haren a sansanonin sojin ƙasar.
Mayaƙan ISWAP sun kai hari sansanin sojin Najeriya a garin Ngoshe, da ke ƙaramar hukumar Gwoza, inda suka kashe aƙalla sojoji tara da kuma wani limamin gari, kamar yadda majiyoyin soji uku suka bayyana da yammacin Laraba.
Maharan dai, waɗanda suka tilasta wa dakarun ja da baya daga sansaninsu, sun ƙwace bindigogi da harsasai sannan suka yi awon-gaba da wasu mata da ba a san adadinsu ba, kamar yadda majiyoyin da ba su yarda a ambaci sunayensu ba saboda ba da su da ikon magana da kafofin watsa labarai a hukumance suka bayyana.
Dakarun da suka jikkata kuma an kai su birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin samun kulawa.