Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMa’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana cewa ba ita ce keda...

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana cewa ba ita ce keda alhakin kashe jagoran koli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda ta ce Isra’ila ce ta kai harin da ya hallaka shi.

Donald Trump ya nesanta Kansas a kidan Shugaban Iran

Babban jami’in kula da manufofi a Pentagon, Elbridge Colby, ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake bayar da shaida a gaban kwamitin kula da harkokin soji na majalisar dattawan Amurka.

Ya ce harin da ya kashe Khamenei da wasu manyan shugabannin Iran ba ya cikin shirin yakin da sojojin Amurka ke gudanarwa.

“Wadannan duk ayyukan Isra’ila ne,” in ji Colby, yana mai mayar da martani ga tambayoyin da ‘yan majalisa suka yi masa kan ko sauya gwamnati a Iran na daga cikin manufofin Amurka.

Salon maganar Colby ya sha bamban da na Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda tun bayan fara hare-haren.

A wani jawabi da ya yi a ranar Asabar, Trump ya ce gwamnatin Iran ta shafe shekaru 47 tana furta kalaman “mutuwa ga Amurka” tare da yin da abin da ya kira zubar da jini da kashe-kashe ba kakkautawa.

A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya ce Khamenei bai iya tserewa daga ingantattun hanyoyin leken asiri da bin diddigin Amurka ba.

Ya kara da cewa, “mun yi aiki kafada da kafada da Isra’ila, babu abin da shi ko sauran shugabannin da aka kashe tare da shi za su iya yi.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments