Kasar Isra’ila ta sanar da dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar bayan ta kai wani hari Iran a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawa da Amurka.
Ministan Tsaron Isra’ila Israel Katz ya bayyana cewa ƙasarsa da haɗin gwiwar Amurka sun kai “hare-haren kandagarki” an Iran, saboda abin da ya kira barazanar da take yi ga tsaron ƙasarsu.
Katz ya kuma ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa baki ɗaya, sannan ya yi kira ga ‘yan ƙasar su bi umarnin rundunar soji ta Home Front Command wadda ke da alhakin kare fararen-hula.
“Ƙasar Isra’ila ta kai harin kandagarki an Iran.
Wasu shaidu sun ce sun ji kara mai karfi na fashewar abubuwa a Tehran, inda hayaƙi ya mamaye sararin samaniya, ko da yake kawo yanzu Iran ba ta yi martani ba.
An ji ƙarar fashe-fashe a Isfahan, Qom, Karaj da Kermanshah, a cewar kamfanin dillanacin labarai na Fars News Agency.
Hare-haren dai na zuwa ne a yayin da ake tattaunawa tsakanin Amurka da Iran sakamakon zaman ɗarɗar kan shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.