Jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi magana da murya guda ɗaya wajen watsi da sabuwar dokar zaɓe da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanyawa hannu, bayan dambarwa a zauren majalisar wakilai da dattijai.
Yayin wata ganawa tsakanin ɓangarorin jam’iyyun adawar na Najeriya da yammacin jiya Alhamis a Abuja fadar gwamnatin ƙasar, jam’iyyun adawar sun kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da hukumomin gwamnati kamar su DSS, ICPC da EFCC wajen musgunawa ƴan adawa.
Cikin ƴan adawar da suka hallara a gaban wannan taro har da tsaffin ƴan takarar shugabancin ƙasa a Najeriyar da suka ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da ya yi takara a jam’iyyar PDP kana Peter Obi da ya yi LP takara.
Sauran sun ƙunshi fitattun ƴan siyasa daga ɓangarori daban-daban na Najeriyar ciki har da tsohon minista Rotimi Amechi da kuma Buba Galadima na jam’iyyar NNPP.
Wannan dai shi ne karon farko da ake ganin makamancin wannan taro tsakanin ɓangarorin ƴan adawar daga mabanbantan jam’iyyun siyasar Najeriyar wanda ake ganin suna ƙoƙarin haɗa ƙarfi ne wajen tunƙarar barazanar jam’iyya mai mulki ta APC.
Akwai dai zarge-zargen cewa gwamnatin Najeriyar na yiwa ƴan adawa ɗauki ɗai-ɗai don kulle bakinsu a gefe guda kuma take barazana ga masu riƙe da madafun iko don mara mata baya bisa tilasci ta hanyar sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki.