Mazauna kauyukan Gwana, Digare, Garin Mansur da Yalo da ke gundumar Gwana a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi sun tsere zuwa jihar Gombe sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Bala Mohammed ta ce za ta yi iya kokarinta wajen kawo karshen rikicin domin al’umma su koma gidajensu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a Facebook cewa ta samu rahoton hare-hare a yankunan kuma ta tura karin dakaru garuruwan.
Rahoto ya nuna cewa hare-haren da aka kai Bauchi shi ne hari na farko wanda ya faru a Digare, inda aka sace mutane shida, yayin da daga baya aka ceto biyu daga cikinsu.
Hari na biyu ya faru a Garin Kwairi, inda aka sace wani kansila tare da mata biyu, ‘yan bindigar sun kuma kai hari a Gwana, inda suka kashe sojoji biyu da dan kungiyar sa-kai guda.