Ƙungiyar AFAN ta manoman Najeriya ta buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, da ya gaggauta tallafa farashin kayan noma, taraktoci da sauran injunan noma domin rage asarar da manoma ke fuskanta.
Shugaban AFAN na ƙasa, Dr. Farouk Rabiu Mudi, ya ce manoma sun yi asarar har kashi 85 cikin 100 na fiye da tan miliyan 50 na amfanin gona bayan girbi a kakar da ta gabata, sakamakon sauyin yanayi da faɗuwar farashi.
Ya kuma koka kan tsadar kayan noma, haraji da kuɗin jigilar kaya daga jihohi da ƙananan hukumomi, rashin daidaiton kuɗi da kuma shigo da arha daga waje, wanda ya ce na rage darajar kayan cikin gida.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci ‘yan majalisa su bai wa fannin noma fifiko domin mayar da shi babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga bayan mai da iskar gas.