Afganistan ta yi Allah-wadai da hare-haren da makwabciyarta Pakistan ta kai wata makarantar addini da kuma gidaje a lardunan Nangarhar da kuma Paktika da ke kan iyakar ƙasashen.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 80 daga ciki har da mata da yara da kuma jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Afghanistan ta fitar, ta ce harin na Pakistan ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma haƙƙin makwabtaka, don haka ta ce nan ba da jimawa ba za ta maida martani akai.
Nezakat mai shekaru 35, ya ce harin ya yi sanadiyar mutuwar ƴaƴansa da mahaifinsa da sauran iyalansa, bayaga gidansa da ya rushe baki ɗaya.
Tuni aka gudanar da jana’izar mutanen da suka rasa rayukansa sanadiyar harin a jiya Lahadi, wacce ta samu halartar ɗinbin mutane.
Wannan shi ne hari mafi muni na baya-bayan nan da aka kai tsakanin Afghanistan da Pakistan, bayan rikicin da suka gwabza a watan Oktoban bara, da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 70 daga ɓangarorin biyu.
Ita Pakistan ta ce ta kai harin ne na kan iyaka, kan wasu ƙungiyoyin ƴan ta’addan da suka kai harin ƙunar baƙin wake cikin ƙasarta.